Alhassan Ɗantata: Ɗan Najeriya da ya je aikin Hajji a jirgin ruwa
Shekaru kimanin 99 kenan da attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka ta yamma a wancan zamanin, Alhaji Alhassan Ɗantata ya gudanar da aikin Haji tare da tawagar mutanen da ya ɗauki nauyi su 15.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaMasana tarihi sun ce Alhaji Alhassan Ɗantata shi ne fitaccen ɗan Najeriya na biyu da ya je aikin Hajji a jirgin ruwa, bayan Sarkin Katsina, Muhammadu Dikko a 1921, abin da ya ɗauki hankalin duniya a zamanin.
Mafi yawancin maniyyata a wancan lokacin na zuwa aikin Hajji ne ta amfani da jakuna da dawaki da raƙuma sannan kuma suna yada zango a ƙasashe da garuruwa kafin su isa Makka.
BBC ta rawaito cewa, Domin kawo muku tarihin aikin Hajjin na marigayi Alhaji Alhassan Ɗantata, BBC ta yi amfani da littafin rayuwar Alhaji Alhassan Ɗantata mai suna “The Life and Times of Alhaji Alhassan Ɗantata, A merchant par exellence“, wanda Hassan Sanusi Dantata ya rubuta.

Alhassan Ɗantata yana da ƴaƴa 65 ciki har da Alhaji Aminu Dantata da Alhaji Sanusi Dantata wanda kaka ne ga Aliko Dangote
