Kamfanin China Ya Kirkiri Na’ura Da Ke Ba Masoya Damar Musayar Kiss Duk Da Nisan Juna

Fasahar zamani na ci gaba da kawo sababbin abubuwa masu ban mamaki.

Wani kamfani daga kasar China ya kirkiri wata na’ura ta musamman da ake cewa tana bai wa masoya masu nisan juna damar yin kiss ta hanyar waya.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

An ce wannan na’ura tana aiki ne da haɗuwa da wayar salula, inda mutum zai iya aika motsin kiss dinsa zuwa ga abokin soyayyarsa da ke wani wuri daban.

Na’urar na kwaikwayon motsin leɓɓa, har ma wasu rahotanni na cewa tana iya kwaikwayon yanayin matsin kiss domin a ji kamar na gaske.

Wannan kirkira ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Wasu na ganin babbar hanya ce ta rage kewar masoya masu soyayyar nesa, musamman ma’aurata ko masu shirin aure da ke rabuwa saboda aiki, karatu ko tafiya.

Sai dai wasu na ganin wannan fasaha na da ban mamaki kuma tana tayar da tambayoyi game da makomar soyayya a zamanin fasaha.

Shin wannan na’ura za ta iya maye gurbin kusanci na hakika tsakanin masoya?

Ko kuwa wata sabuwar hanyar nishadi ce kawai da ba za ta dade ba?

Kai me kake tunani game da wannan sabon kirkira?

Shiga Nan Don Samun Wasu Sirrikan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *