Dalilai 7 Da Yasa Ba A Son A Ci Naman Da Bai Gama Dahuwa Ba

A lokacin Sallah mutane da yawa suna son cin nama kai tsaye daga wuta, amma masana lafiya suna gargadin cewa cin naman da bai gama dahuwa ba na iya jawo matsaloli ga lafiya.

Ga wasu daga cikin dalilan da yasa ake bada shawarar a tabbatar nama ya dahu sosai kafin a ci.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

1. Yana Iya Ɗauke Da Ƙwayoyin Cuta

Naman da bai dahu sosai ba na iya ƙunsar ƙwayoyin cuta kamar Salmonella da E. coli waɗanda ke haddasa amai, gudawa da matsanancin ciwon ciki.

2. Yana Iya Kawo Tsutsotsi A Jiki

Wasu nau’in nama idan ba su dahu sosai ba suna iya ɗauke da ƙwayoyin tsutsa da ka iya shiga jikin mutum su haddasa matsala.

3. Yana Iya Jawo Ciwon Ciki Mai Tsanani

Cin É—anyen nama ko wanda bai dahu sosai ba kan haddasa kumburin ciki, tashin zuciya da matsalar narkewar abinci.

4. Hadarin Guba Daga Abinci

Food poisoning na daga cikin manyan matsalolin da naman da bai dahu sosai ba ke haifarwa, musamman idan ba a kula da tsafta wajen sarrafa naman ba.

5. Yana Da Wahalar Narkewa

Naman da bai dahu sosai ba yana iya zama mai wahalar narkewa, musamman ga masu fama da ulcer ko wasu matsalolin ciki.

6. Yana Iya Cutar Da Masu Ƙaramin Garkuwar Jiki

Yara, mata masu ciki da tsofaffi sun fi fuskantar haɗari idan suka ci naman da bai dahu sosai ba saboda jikinsu baya iya yaƙar ƙwayoyin cuta cikin sauƙi.

7. Zai Iya Rage Amfanin Sinadaran Abinci

Dahuwa mai kyau na taimakawa jiki ya fi anfani da sinadaran protein da ke cikin nama cikin sauƙi da lafiya.

Domin kare lafiyarka da ta iyalinka, yana da kyau a tabbatar an dafa ko an soya nama yadda ya kamata kafin a ci shi.

Duba Karin Bayani

📢 Kada ka tsaya anan!

👉 Danna nan ka ga abin da ke gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *