Alamomi 9 Da Ke Nuna Kusantowar Jinin Al’adar Mace

Jinin al’ada abu ne na dabi’a da ke faruwa ga mata a kowane wata.

Kafin lokacin ya zo, jikin mace kan fara nuna wasu alamomi da suke sanar da cewa lokacin al’ada ya kusa.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Ga wasu daga cikin alamomin da aka fi gani:

1. Ciwon Mara

Mata da dama kan fara jin ciwo ko nauyi a ƙasan ciki kafin jinin al’ada ya fara.

2. Ciwon Baya

Wasu mata kan ji ciwo a baya musamman ƙasan baya kwanaki kafin al’ada.

3. Sauyin Yanayi

Fushi, damuwa ko yawan jin haushi na daga cikin abubuwan da mata ke fuskanta kafin jinin al’ada.

4. Jin Gajiya

Jiki kan yi nauyi kuma mace ta rika jin kasala ko rashin kuzari.

5. Kumburin Nono

Nono kan yi tauri ko ya fara ciwo saboda sauyin hormones a jiki.

6. Yawan Jin Yunwa

Wasu mata kan fara jin sha’awar cin wasu abinci musamman masu zaki ko kayan marmari.

7. Kuraje A Fuska

Sauyin hormones kan sa wasu mata samun pimples ko kuraje kafin al’ada.

8. Canjin Fitsari Ko Fitar Ruwa

Wasu mata kan lura da karin ruwa daga gaba ko sauyin yanayin jikinsu.

9. Ciwon Kai

Yawan ciwon kai ko jiri na iya kasancewa daga cikin alamomin kusantowar al’ada.

Duk da cewa alamomin suna bambanta daga mace zuwa mace, yana da kyau mace ta san yadda jikinta yake domin kula da lafiyarta.

Idan alamomin suka yi tsanani sosai ko suka zama ba daidai ba, yana da kyau a tuntubi likita.

Duba Karin Bayani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *