Aure ba zama kawai bane ko cika al’ada ba. Aure yana buƙatar hikima, kulawa, da kuma ƙoƙarin faranta ran juna a tsakanin ma’aurata.

Maganar da ake yi cewa mace ta zama mai iya jan hankalin mijinta a gida, ba tana nufin rashin mutunci ba ne.

A’a, ana nufin mace mai salo, nishadi, da kuma sanin yadda za ta kula da aurenta cikin hikima.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

—

1. Ki Zama Mai Salo a Gare Shi

Kada kullum ya ganki a yanayi guda.
Sauya kaya, amfani da turare mai dadi, da gyara jiki na sa mijinki ya riƙa jin sabuwar sha’awa a gare ki.

—

2. Ki Nuna Soyayya Ba Tare Da Kunaya Ba

Ƙananan abubuwa kamar:

runguma

murmushi

kalamai masu dadi

na iya ƙara masa farin ciki da kusanci a tsakaninku.

—

3. Ki Zama Mai Wasa da Raha

Ba kullum tsanani bane.
Wani lokaci kiyi wasa da shi cikin nishadi domin ƙara soyayya da kusanci.

—

4. Ki Fahimci Abubuwan Da Yake So

Ki lura da abubuwan da yake so, ki kuma yi ƙoƙarin faranta masa rai cikin tsafta da mutunci.

Fahimtar juna na da matuƙar muhimmanci a aure.

—

5. Ki Kula da Tsafta da Kamshi

Tsafta da ƙamshi na daga cikin abubuwan da ke jan hankali sosai.
Miji yana jin daɗin mace mai kula da jikinta.

—

6. Ki Zama Abokiyar Rayuwarsa

Ba wai mata kawai ba, ki zama:

abokiya

mai sauraro

mai ba da shawara

Wannan yana ƙara dankon zumunci sosai.

—

7. Ki Riƙa Masa Kalaman Dadi

Kalaman kirki na da tasiri sosai.
Kalma ɗaya mai kyau daga gare ki na iya sauya masa yanayi gaba ɗaya.

—

Muhimmin Abu

Duk waɗannan abubuwa ana yin su ne a tsakanin mace da mijinta kawai.

Wannan shi ne halal, kuma yana daga cikin sirrin da ke sa aure ya kasance mai daɗi da ɗorewa.

—

Ki kasance mace mai mutunci a waje, amma a cikin gidanki ki zama mace mai salo, mai kulawa, da mai faranta ran mijinki.

Wannan yana daga cikin sirrin zaman aure mai dadi.

—

Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *