A cikin soyayya ko aure, akwai wasu halaye da namiji ke yi da kan sa mace ta fara gajiya da shi, ko da kuwa tana sonsa sosai.

Fahimtar waɗannan abubuwa na taimakawa wajen gyara kuskure da ƙara dankon zumunci.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

1. Rashin Kulawa

Mace tana son kulawa da attention. Idan namiji ya daina nuna kulawa, kira, ko tambayar halinta, hakan na sa ta fara jin an watsar da ita.

2. Rashin Girmamawa

Idan namiji baya girmama mace:

a magana

a mu’amala

zata fara rasa jin daɗin kasancewa tare da shi.

3. Rashin Sadarwa

Rashin yin magana mai ma’ana yana kawo nisa a zuciya. Idan ba a tattauna ba, fahimta zata ragu.

4. Yawan Karya Alkawari

Idan namiji baya cika alkawari, mace zata fara rasa yarda da shi.

5. Rashin Nuna Soyayya

Ko da tana sonsa, idan baya nuna soyayya:

kalamai masu dadi

kulawa

lokaci

zata fara gajiya a hankali.


Soyayya tana bukatar kulawa, girmamawa, da sadarwa.

Idan namiji ya kula da waɗannan abubuwa, zai iya gujewa sa mace ta gaji da shi, kuma soyayya zata ci gaba da ƙarfi.

Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *