“Wani Lokaci Mace Bata Bukatar Kudi… Ga Abunda Mata Suke So” 😭❤️

Mutane da yawa suna tunanin duk abin da mace take bukata daga namiji kudi ne ko gifts masu tsada.

Eh gaskiya kudi yana da muhimmanci a rayuwa… amma akwai wasu abubuwa da suke shiga zuciyar mace fiye da kudi.

Wani lokaci mace bata bukatar ka kashe mata miliyoyi… tana bukatar abubuwa masu sauki amma masu taba zuciya 🥺👇

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

1. Kulawa ❤️

Mace tana son namiji da yake tuna ta.

Ko message ne kawai da safe:

“Kin tashi lafiya?” “Kinci abinci?”

Wadannan kananan abubuwa suna saka mace jin cewa tana da muhimmanci.

2. Lokaci ⏰

Akwai mata da yawa da zasu fi farin ciki idan ka bata lokaci fiye da ka tura mata kudi kawai.

Saboda lokaci yana nuna cewa kana son kasancewa tare da ita.

3. Gaskiya 🤍

Karya tana kashe soyayya a hankali.

Mace tana son namiji wanda zata iya trust dinsa ba tare da tsoro ko overthinking ba.

4. Attention 😭

Wani lokaci mace zata yi shiru amma tana son ka lura da canjinta.

Idan tana cikin damuwa tana son ka tambaye ta:

“Me yake damunki?”

Ba wai ka bar ta tana ta tunani ita kadai ba.

5. Kalmomi Masu Dadi 💕

Mace tana son jin:

“Ina sonki.” “Kin yi kyau.” “Ina alfahari dake.”

Kalaman soyayya suna iya gyara ran mace fiye da yadda mutane suke tunani.

6. Respect 🙏

Babu abin da yake saka mace jin dadin soyayya kamar namiji mai girmamawa.

Yadda yake magana da ita, yadda yake kare mutuncinta da yadda yake mu’amala da ita a gaban mutane… duk suna da muhimmanci sosai.

7. Peace Of Mind 🥹

Gaskiya mafi yawan mata basa neman perfect man…

Suna neman namiji wanda zai basu kwanciyar hankali.

Wanda ba zai saka su kuka kullum ba.

Wanda idan suna tare dashi zuciyarsu zata samu nutsuwa.

Karshe… ❤️

Eh kudi yana da amfani… amma wani lokaci mace zata fi son namiji mai kulawa da gaskiya fiye da wanda yake da kudi amma babu soyayya.

Saboda:

“Zuciyar mace tana son wanda zai kula da ita, ba wanda zai nuna mata kudi kawai ba.” 😭❤️

Duba Karin Bayani A Nan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *