Soyayya Ko Yaudara? Yadda Za Ka Bambance Gaskiya Da Ƙarya A Soyayya
Soyayya abu ce mai dadi idan ta kasance ta gaskiya. Amma a wannan zamani, mutane da yawa suna shiga soyayya ne da niyyar anfani, wasa da zuciya ko yaudara.
Wasu suna nuna kulawa da kauna a farko, amma daga baya sai a gano cewa duk abin da suke yi yaudara ce kawai.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaTo ta yaya mutum zai gane tsakanin soyayya ta gaskiya da kuma karya?
Mutumin da yake sonka da gaske baya tunanin anfani kawai. Zai kula da damuwarka, mutuncinka da farin cikinka ba tare da wata boyayyiyar manufa ba.
Idan mutum kullum anfani yake nema a wajenka, musamman kudi ko wasu bukatu, amma baya nuna kulawa idan kai ne cikin matsala, akwai yiwuwar ba soyayya bace ta gaskiya.
A soyayya ta gaskiya akwai gaskiya da amana. Wanda yake sonka da gaske baya yawan karya, boye abubuwa ko rikita magana.
Amma idan kana yawan kama shi da karya, alkawarin banza da canza hali lokaci-lokaci, hakan na iya zama alamar yaudara.
Haka kuma, soyayya ta gaskiya tana kawo kwanciyar hankali. Ko da akwai sabani, zaka ji cewa mutum yana kokarin gyara alaka.
Amma idan kullum cikin kuka, damuwa da rashin tabbas kake, akwai bukatar ka sake tunani akan alakar.
Mutum mai gaskiya baya jin kunyar bayyana ka a rayuwarsa. Zai mutunta ka a gaban mutane kuma ya tsaya tare da kai a lokacin wahala.
Amma mai yaudara yawanci sai idan yana bukata yake neman ka, sannan ya bace idan komai ya daidaita.
Wani babban kuskure da mutane da yawa suke yi shine watsi da alamun gargadi saboda tsananin so.
Idan zuciyarka tana gaya maka akwai matsala, kada kayi watsi da hakan. Ka lura da yadda mutum yake mu’amala da kai, ba wai kalamansa kadaai ba.
Soyayya ta gaskiya tana tare da mutunci, amana, hakuri da kulawa. Yaudara kuma tana tare da karya, anfani da wasa da zuciya.
Don haka kafin ka mika zuciyarka gaba daya ga wani, ka tabbatar kana kallon halayensa ba kalamansa kawai ba.
