Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wasu ‘yan Kannywood biyu mace da namiji
Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da jaruman masana’ntar shirya finafinai ta Kannywood biyu, Adam Garba (Raba-Gardama) da Amina Uba Hassan (wadda tsohuwar matar jarumi Adam A. Zango ce), daga gudanar da harkokin fim a Jihar Kano har tsawon shekara guda.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaSanarwar da hukumar ta fitar ta hannun jami’in hulda da jama’a Abubakar Sani ta ce an É—auki matakin ne bayan bayyanar jaruman biyu a wani bidiyo da ta bayyana a matsayin wanda ya saÉ“a da tarbiyya, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Jihar Kano.
Sai dai wani bidiyo na jarumi Adam A Zango dake yawo a kafafen sadarwa, ya nuna cewar Adam na farin ciki da wannan dakatarwarda akayiwa Amina Uba Hassan wanda tsohuwar matar sa ce.
