Yadda Aka Yi Wa Matashi Bulala 20 Bayan An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin Shekara 13 Kan Yi Wa Ƙaramar Yarinya Fyade — Kalli Bidiyo
Wata kotu a Jihar Neja ta yanke wa wani matashi mai suna Aliyu Bala hukuncin ɗaurin shekara 13 a gidan yari bayan ta same shi da laifin yi wa wata yarinya mai shekaru 10 fyade.
Baya ga ɗaurin, kotun ta kuma umarci a yi wa Bala bulala 20 a bainar jama’a, tare da biyan diyya ta ₦250,000 ga yarinyar da aka zalunta.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaBayan yanke hukuncin, an kai Bala fadar Hakimin Bosso, inda aka aiwatar da hukuncin bulalar a bainar jama’a a gaban jama’ar gari.
Daraktar-Janar ta Hukumar Kare Haƙƙin Yara ta Jihar Neja, Barrister Ummul-Kalthume Muhammad, ta bayyana hukuncin a matsayin wani abu da ba kasafai ake gani ba.
Ta ce hukuncin ya nuna cewa gwamnatin jihar ba za ta yi wasa da laifukan cin zarafin yara ba.
A cewarta, hukuncin bulalar a bainar jama’a na daga cikin matakan da ake son amfani da su wajen aika saƙo mai ƙarfi ga duk wanda ke tunanin zai iya cin zarafin yara ba tare da fuskantar hukunci ba.
Hukumar ta kuma bayyana cewa hukuncin ba wai ga wanda aka samu da laifin kaɗai yake zama darasi ba ne, illa ma saƙo ne ga al’umma cewa cin zarafin yara babban laifi ne kuma masu aikata irin wannan laifi za su iya fuskantar hukunci a ƙarƙashin doka.
Me kuke tunani game da wannan hukunci?
Shin kuna ganin irin wannan hukunci zai taimaka wajen rage cin zarafin yara?
Ku kalli bidiyon da ke ƙasa domin ganin yadda abin ya faru.
