Bidiyon Amal Umar Ya Jawo Cece-kuce A Kafafen Sada Zumunta
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna jarumar Kannywood yayin bikin Sign Out dinta bayan kammala karatun digiri, lamarin da ya jawo ra’ayoyi mabambanta daga mutane.
A cikin bidiyon, an ga wani matashi yana yi mata rubutu na taya murnar kammala karatu a jikinta, abin da wasu suka dauka a matsayin nishadi da al’adar Sign Out, yayin da wasu kuma suke ganin bai dace ba musamman ga ‘ya mace musulma mai tarbiyya.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa
Wasu daga cikin masu sharhi sun bayyana cewa irin wannan abu na iya jawo magana a media saboda yadda mutane ke kallon rayuwar fitattun mutane, musamman wadanda suke da tasiri ga matasa.
Sai dai wasu sun kare ta, suna cewa bikin Sign Out yana zuwa da salo daban-daban kuma bai kamata a rika yanke hukunci cikin gaggawa ba kan kuskuren da mutum zai iya yi sau daya.
Duk da cece-kucen da ake yi, mutane da dama sun yi mata fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya sa ilimin da ta samu ya amfani rayuwarta da makomarta.
Kalla Bidiyo A Kasa

