Ga Abunda Ya Kamata Ku Sani Game Da Iskar Da Ke Fita Daga Farjin Mace Lokacin Saduwa
A wasu lokuta yayin saduwa ko bayan an gama jima’i, mace na iya jin wata iska tana fita daga gabanta kamar sautin tusa.
Wannan abu yana yawan tayar da tambayoyi da damuwa ga wasu mata, musamman wadanda basu san dalilin faruwarsa ba.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaMasana da malamai sun bayyana cewa wannan iska ba lallai tana nufin wata cuta ko matsala mai hatsari ba.
Yawanci tana faruwa ne lokacin da iska ta shiga cikin farji yayin motsi ko saduwa, sannan daga baya ta rika fita yayin canza yanayi ko motsi.
A bangaren ilimin addini, malamai sun yi sabani kan hukuncin wannan iska ko tana karya alwala ko a’a.
Mazhabar Hanafiyya da Malikiyya sun bayyana cewa irin wannan iska ba ta karya alwala, domin ba daga dubura take fitowa ba, kuma babu nassi karara da ya tabbatar da hakan.
Sai dai Mazhabar Shafi’iyya da Hanabila sun tafi akan cewa duk wani abu da ya fita daga gaba ko baya yana karya alwala, saboda sun yi kiyasin ta da tusa.
Saboda haka, wasu malamai suna ganin mafi alheri mace ta sake alwala idan hakan ya faru domin fita daga sabanin malamai, musamman idan tana son yin ibada cikin natsuwa.
A bangaren lafiya kuma, wannan iska tana yawan faruwa ga mata da dama kuma ba wani abin kunya bane.
Wasu mata suna fuskantar hakan fiye da wasu saboda yanayin halittar jikinsu ko irin motsin da ake yi yayin saduwa.
Haka kuma wasu masana suna cewa kula da tsaftar jiki da yin atisaye na gyaran ƙasan mara na iya taimakawa wajen rage yawan faruwar hakan.
Abu mafi muhimmanci shi ne kada mace ta shiga tsananin damuwa idan hakan ya faru lokaci zuwa lokaci, domin a mafi yawan lokuta ba wata babbar matsala bace ta rashin lafiya.
Wallahu A’alam.
