🔥 APC Ta Gudanar Da Zaɓukan Fidda Gwani Na Majalisar Tarayya A Katsina Cikin Lumana Da Kwanciyar Hankali

A yau Asabar ne jam’iyyar (APC) ta gudanar da zaɓukan fidda gwani ta hanyar sasanci a dukkan mazaɓun Majalisar Tarayya guda 15 na jihar cikin kwanciyar hankali da lumana.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Membobin jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar sun fito domin nuna goyon baya da amincewarsu ga tsarin sasancin da jam’iyyar ta aiwatar, kamar yadda dokokin zaɓe suka tanada.

Yayin kaddamar da tabbatar da ‘yan takarar mazaɓar Rimi, Charanchi da Batagarawa, gwamnan jihar ya bayyana jin daɗinsa bisa yadda aka gudanar da tsarin cikin haɗin kai da fahimtar juna.

Gwamnan ya ce wannan ya nuna ƙarfin jam’iyyar APC da kuma yadda take da tagomashi a faɗin jihar, yana mai jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da inganta rayuwar al’umma.

Shi ma shugaban APC na jihar Katsina, ya bayyana cewa jam’iyyar ta zaɓi tsarin sasanci ne domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin ‘ya’yanta da kuma tabbatar da samun gagarumin nasara a babban zaɓe mai zuwa.

Ya kuma bayyana cewa an gudanar da tsarin ne a gaban wakilan uwar jam’iyyar daga Abuja tare da wakilan hukumar zaɓe domin tabbatar da sahihancin tsarin kamar yadda doka ta tanada.

Dubban magoya baya da masu ruwa da tsaki daga mazaɓu 361 na jihar Katsina ne suka halarci wannan taro tare da amincewa da ‘yan takarar Majalisar Tarayya guda 15 na jam’iyyar APC.

Ga jerin wasu daga cikin ‘yan takarar da aka tabbatar:

• Hon. Usman Murtala Banye — Rimi/Charanchi/Batagarawa
• Hon. Abba Dahiru Barau Mangal — Katsina Ta Tsakiya
• Hajiya Jamila Abdu Mani — Bindawa/Mani
• Hon. Yusuf Buhari — Daura/Mai’adua/Sandamu
• Hon. Sada Soli — Jibia/Kaita
• Hon. Yau Nowa — Funtua/Dandume
• Hon. Aminu Balele — Dutsinma/Kurfi
• Hon. Hamza Sule Faskari — Kankara/Sabuwa/Faskari
• Hon. Abdullahi Dabai — Bakori/Danja

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da dukkan matakan zaɓen cikin lumana ba tare da wata matsala ba, lamarin da ya ƙara nuna haɗin kai a cikin jam’iyyar APC a jihar Katsina.

Duba Karin Bayani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *