Yadda Zaka Yi Wa Mace Magana Ta Tsaya Ta Saurare Ka (Ba Tare Da Ka Rude Ba)
Dayawa daga cikin maza sukan tsinci kansu cikin halin fargaba da rudani a duk lokacin da bukatar hakan ta taso na su tunkari mace domin gabatar da kansu.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaWannan fargabar takan sa kalaman da mutum ya dade yana tsarawa a ransa su bace, ko kuma ya gaza fadar su yadda ya kamata.
Idan kana daya daga cikin wadanda suke fuskantar wannan kalubalen, ga wasu muhimman shawarwari da zasu taimaka maka:
1. Daina Tsara Kalaman Cikin Zuciya
Ka sani, wadancan kalaman da kake ta faman tsarawa a zuciyarka kafin ka karasa gun mace, ba abinda zasu haifar maka face rashin kwarin gwiwa.
Idan ka cika kanka da dogon bayani a ranka, da zaran ka tsaya a gabanta, sai kaga kalaman sun gudu, hakan kuma zai sa ka fara zazzare ido.
2. Kwarin Gwiwa Ya Fi Kalaman Burge-Duniya
Zaka ga namiji ya iya tsara magana sosai idan yana cikin abokansa, amma da zaran ya tunkari mace sai ya fara in-ina.
Abinda kake bukata ba wai yawan kalamai ba ne, kwarin gwiwa (Confidence) ne.
- Kada ka kokarta nuna kwarewa ko kokarin fasa mata kai da kalaman dadin baki.
- Yin hakan yakan sa mutum ya “kwafsa” tun kafin ya yi nisa.
3. Yi Magana Cikin Nutsuwa
Mata suna yanke wa namiji hukunci ne ta yanayin nutsuwarsa, ba wai ta yawan kalaman da ya iya tsara wa ba.
“Idan kana son darajarka ta karu a idon mace, ka bayyana mata abinda yake ranka cikin kwanciyar hankali ba tare da kokarin burge ta ba.”
4. Ka Kasance Mai Saukin Kai (Be Natural)
Kuskuren da maza ke yi shi ne tsara “Script” a ransu. Idan ka tsara abinda zaka gaya mata tsaf, to kana haduwa da ita zaka rikice.
Me ya sa? Domin a cikin kalaman da ka tsara, ba ka tanadi amsar tambayar da zata iya jefo maka ba.
Idan ta jefa maka tambayar da ba ka yi tsammani ba, anan ne zaka ga namiji ya rude domin bayani ya kare.
Sakon Karshe Zuwa Ga Maza
Mata suna son namijin da ya san abinda yake yi kuma yake magana kai-tsaye daga zuciyarsa.
Ka rage fargaba, ka kara nutsuwa, sannan ka zama kanka. Wannan shi ne sirrin da zai sa mace ta tsaya ta saurare ka da dukkan hankalinta.
Maza a kula!
Kuna iya barin ra’ayoyinku a sashen sharhi (comments), sannan kada ku manta ku raba wannan rubutun (share) ga abokanku.
