Zargin Bidiyon Da Ya Haddasa Cece-kuce A Kafafen Sadarwa – Zulaihat Ta Yi Bayani
A kwanakin nan kafafen sada zumunta sun cika da wani bidiyo da ya jawo cece-kuce sosai, inda ake ganin wani saurayi da budurwa a cikin wani hali da ya tayar da hankulan mutane.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaA karon farko, budurwar da ake kira Zulaihat ta fito ta yi magana, inda ta bayyana cewa abin da ya faru ba yadda mutane ke yadawa ba ne, kuma ba ta kasance cikin hayyacinta sosai a lokacin da abin ya faru.
Yadda Labarin Ya Fara
Zulaihat ta bayyana cewa ta fara sanin saurayin ne ta hanyar soyayya ta yau da kullum, inda ya dade yana nuna mata kulawa da sha’awa amma bata fara bashi dama ba a farko.
Daga baya, ta ce saurayin ya zo daga Kano zuwa Kaduna domin ganawa da mahaifiyarta, inda aka karbe shi a gidan su kuma aka sansance shi a matsayin wanda suke hulda da ‘yar su.
Bayan haka ne soyayyarsu ta fara shiga tsakaninsu sosai, har suka fara yawan haduwa.
Ranar Abin Da Ya Faru
A cewarta, wata rana saurayin ya ce zai zo Kaduna su fita yawo, amma ta sanar da shi cewa ba ta saba fita yawo ba, daga makaranta sai gida.
Sai dai daga baya ya zo makarantar ta, ya dauke ta, suka je waje cin abinci, sannan suka ci wani abu tare kafin daga bisani abin ya rikide ya dauki wani sabon salo wanda ya jawo cece-kuce.
Zulaihat Ta Ce Me Ya Faru?
Zulaihat ta bayyana cewa abin da ya faru ya faru ne a yanayin da ba ta da cikakken hankali ko nutsuwa, tana kuma jaddada cewa wasu abubuwan da ake yadawa a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne kamar yadda ake tunani.
Kira Ga Jama’a
Masana da dama sun yi kira ga jama’a da su daina yanke hukunci da gaggawa kan irin wadannan batutuwa har sai an kammala bincike, tare da jaddada muhimmancin kulawa da lamuran yarda (consent) da kuma gujewa yada bidiyo ko jita-jita da ka iya cutar da mutane.
