Screenshot

Yadda Suka Daura Aure A TikTok Sabida Gudun Aikata Zina… Kalla Bidiyon A Kasa

Batun auren wasu matasan TikTok da aka fi sani da “Yaran Kano” da “Ummiter” ya dauki hankalin mutane sosai a kafafen sada zumunta, musamman bayan wani bidiyo ya bayyana inda aka nuna ana gudanar da wani yanayi irin na daurin aure.

Screenshot

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Tun bayan fitowar bidiyon, mutane suka fara tambayar ko da gaske auren suka yi ko kuma content ne kawai domin daukar hankali da kara trending.

Sai dai matasan sun bayyana cewa auren nasu gaskiya ne ba wasan kwaikwayo ko content ba.

Duk da haka, har yanzu mutane da dama musamman a Arewa suna ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabambanta akan lamarin.

Wasu na ganin cewa matasan sun dauki mataki mai kyau domin kaucewa aikata abin da bai dace ba, yayin da wasu kuma ke ganin abubuwan da suka saba nunawa a baya sun sa mutane suka kasa yarda da su cikin sauki.

A gefe guda kuma, akwai masu cewa matsalar ita ce yadda ake yawan sukar duk wanda ya fara haskawa ko samun karbuwa a kafafen sada zumunta.

Wasu na ganin akwai tsana da rashin yarda da sabbin salon rayuwar matasa, musamman idan suka shahara cikin kankanin lokaci.

Screenshot

Sai dai wasu kuma sun jaddada cewa idan har matasan sun ce aurensu gaskiya ne kuma an cika sharuddan aure kamar waliyyai da sadaki, to babu dalilin ci gaba da zargin su ba tare da hujja ba.

A cikin bidiyon da ya kara yaduwa, an hangi matasan zaune tare da wasu mutane da suka bayyana a matsayin waliyyai, inda aka ce an biya sadaki kuma aka amince da auren.

Screenshot

Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai a yanar gizo yayin da mutane ke ci gaba da bayyana ra’ayoyi daban-daban akan wannan batu mai daukar hankali.

Kalla cikakken bidiyon domin ganin yadda komai ya faru👇

Screenshot
Screenshot

Kalla Bidiyo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *