Sakonnin Soyayyan Barka Da Sallah Mai Taba Zuciya Da Za Ka Turawa Masoyiyarka

1.

“Barka da Sallah masoyiyata. Allah ya sa farin cikin da kike bani kullum ya dawo gare ki sau dubu.”

2.

“A wannan rana ta Sallah, addu’ata ita ce Allah ya ci gaba da haɗa zuciyoyinmu cikin ƙauna da fahimta.”

3.

“Barka da Sallah ga wacce take saka murmushi a fuskata ko da bana cikin yanayi mai kyau.”

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

4.

“Ko mutane nawa zan gani a Sallah, babu wacce zuciyata take nema kamar ke.”

5.

“Allah ya sa wannan Sallah ta zama mafari na farin ciki, soyayya da albarka a tsakaninmu.”

6.

“Barka da Sallah baby ta. Ki ci kyau, ki yi kyau, amma ki tuna akwai wanda zuciyarsa take wajenki kullum.”

7.

“Ranar Sallah tana min kyau ne saboda ina da wacce zan tura sakon soyayya mai taba zuciya kamar ke.”

8.

“Duk takalmi da kayan Sallah ba su kai kyawunki daukar hankali ba a idona.”

9.

“Allah ya karɓi ibadunmu, sannan ya kare mana soyayyar da take tsakaninmu.”

10.

“Barka da Sallah masoyiyata. Ina fatan wata rana zan kasance tare da ke muna yin bikin Sallah a gida ɗaya.”

11.

“Ko da nisan dake tsakaninmu, zuciyata tana jin kamar kina kusa da ni yau saboda irin son da nake miki.”

12.

“Na gode da kasancewa farin cikina. Barka da Sallah ga mafi muhimmiyar mace a rayuwata.”

Duba Karin Bayani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *