Zuwa gare ku sabbin ma’aurata (shekara 1 zuwa 5) da kuma masu niyyar aure nan kusa, ku sani cewa:

Dukkan ku ‘yan koyo ne a makarantar aure.

Abin da kuka sani ko kuka ji kafin aure, ba lallai ba ne ku same shi daidai a rayuwar aurenku.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Dalili kuwa shi ne:
Kai daban ne, ita ma daban ce, kuma aurenku ba zai zama daidai da na kowa ba.

Muhimmancin Haƙuri da Fahimtar Juna

Ku kasance masu haƙuri da kuma yima juna uzuri, domin ku duka kuna koyon yadda ake tafiyar da rayuwar aure ne a hankali.

Sako Zuwa Ga Miji

Ya kai miji, ka sani cewa matar da ka aura ba ta saba da kula da gida gaba ɗaya ba.

A gidansu, akwai abubuwa da mahaifiyarta ke yi waɗanda ita ba ta taɓa yin su ba ko koyon su sosai ba.

Yanzu ne lokacin da za ta fara:

Koyon kula da gida

Fahimtar yadda ake mu’amala da miji

Koyon yadda za ta nuna soyayya da tausayi

Koyon yadda za ta warware matsaloli

Saboda haka, ka kasance mai haƙuri da ita idan ta yi kuskure, domin koyo ne take yi a hankali.

Sako Zuwa Ga Mace

Ke ma ya kamata ki fahimta cewa mijin da kika aura shi ma ɗan koyo ne.

Kafin aure:

Bai saba da daukar nauyin gida gaba ɗaya ba

Bai saba da kula da mace da iyali kai tsaye ba

Yanzu ne zai fara koyon:

Daukar alhakin gida

Yanke shawara

Warware matsaloli

Kula da ke da iyalinku

Saboda haka, ki ba shi lokaci da haƙuri domin ya koya.

Aure Kamar Girman Yaro Ne

Rayuwar aure kamar tarbiyyar yaro take:

Da farko ana koyon zama

Sannan a fara rarrafe

A riƙa faɗuwa ana tashi

A koya tsayuwa

Daga bisani a fara tafiya

Haka ma aure yake:
A hankali ake koyo, a hankali ake gyarawa, har a kai ga kwarewa.

Ko bayan kun kware, hakan ba zai hana samun ƙalubale ba. Amma muhimmanci shi ne:

Ku yi haƙuri

Ku koyi darasi

Ku ci gaba da tafiya tare

Aure Makaranta Ce

Kada ku manta:
Aure makaranta ce wadda babu ranar kammalawa.

Kullum akwai sabon darasi:

Sabon fahimta

Sabon jarrabawa

Sabon gyara

Idan kuka rungumi haƙuri, fahimtar juna, da soyayya, za ku samu nasara a rayuwar aurenku.

Domin aure ba a kwarewa a rana ɗaya ba, ana koyonsa ne a tsawon lokaci.

Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *