Rashin Karfin Mazakuta Ko Rashin Tashi Da Safe: Ga Abinda Masana Suka Bayyana
Masana lafiya sun bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da ke nuna lafiyar tsarin jikin namiji shi ne yadda gaba ke tashi da safe bayan farkawa daga barci.
Wannan abu dabi’a ce da ke faruwa ga mafi yawan lafiyayyun maza saboda yadda hormones da yawo da jini ke aiki yayin barci.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaA cewar masana, yawanci namiji kan iya samun tashiwar gaba da safe na wasu mintuna, musamman bayan sallar asuba ko lokacin farkawa daga bacci.
Amma idan mutum ya lura cewa hakan ya daina faruwa gaba daya ko kuma yana fama da matsalar rashin karfin mazakuta akai-akai, yana da kyau ya kula da lafiyarsa domin hakan na iya nuna wata matsala a jiki.
Ga wasu daga cikin abubuwan da kan haddasa matsalar rashin karfin mazakuta ko rashin tashi da safe:
• Yawan damuwa da tunani
Yawan stress da damuwar rayuwa na iya rage yadda jiki ke aiki musamman a bangaren hormones da sha’awa.
• Rashin isasshen bacci
Idan mutum baya samun hutu da bacci mai kyau, hakan na iya shafar lafiyar jiki da karfin mazakuta.
• Hawan jini da ciwon siga
Wasu cututtuka kamar hawan jini da diabetes na iya rage yawo da jini yadda ya kamata zuwa gaba.
• Shan taba da abubuwa masu illa
Masana sun bayyana cewa taba sigari, miyagun abubuwa da yawan barasa na iya haddasa matsalar rashin karfi.
• Rashin motsa jiki
Zama babu motsa jiki na tsawon lokaci na iya rage lafiyar jini da kuzarin jiki gaba daya.
• Matsalar hormones
Raguwar wasu hormones musamman testosterone na iya haddasa matsalar sha’awa da rashin karfi.
Masana lafiya sun jaddada cewa kula da lafiyar jiki yana da matukar muhimmanci wajen kare namiji daga irin wadannan matsaloli.
Cin abinci mai kyau, rage damuwa, motsa jiki akai-akai da samun isasshen bacci na taimakawa sosai.
Haka kuma, idan matsalar ta dade tana faruwa, yana da kyau mutum ya nemi shawarar likita domin gano ainihin matsalar maimakon amfani da magunguna barkatai ba tare da shawarar kwararru ba.
Lamarin dai ya sa mutane da yawa fara kara kula da lafiyarsu bayan da masana suka bayyana cewa wasu kan yi watsi da irin wadannan alamomi har sai matsalar ta tsananta.
