A cikin rayuwar aure, sanin halayen matar da za ka aura yana da matuƙar muhimmanci.
Ba a so mutum ya yi aure sannan ya gano wasu halaye da za su kawo rikici a gaba.
Ga wasu abubuwa guda shida (6) da ya kamata ka lura da su kafin ka amince da aure:
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa1. Gwajin Talauci
Ka nuna mata cewa kasuwancinka ya fadi ko an sace maka dukiyarka, ko kuma ba ka da kudi a yanzu.
Ka lura da halinta: shin kulawarta za ta ragu ko za ta ci gaba da baka karfin gwiwa da goyon baya? Mata masu fahimta da rikon gida sukan ci gaba da nuna kulawa.
2. Gwajin Fushi
Ka dan bata rai a kan wani karamin abu.
Ka lura da bakinta: shin tana zagi ko cin mutunci, ko tana kame kanta? Mata masu halin kirki sukan nuna hakuri da ladabi yayin fushi.
3. Gwajin Rike Sirri
Ka fada mata wani babban sirri (na karya), ka nuna mata kar ta bayyana ga kowa.
Idan ta bazama labarin ga abokai ko dangi, hakan na nuna rashin iya rike sirri, wanda zai iya jawo matsala a gida.
4. Gwajin Biyayya
Idan tana son zuwa wani wuri da ta dade tana shiri, ka nuna mata baka son ta je.
Ka lura da halinta: idan ta gamsu da shawarar ka, tana da biyayya. Idan ta nuna rashin jituwa ko ƙiyayya, ka yi hankali.
5. Gwajin Kwadayi
Maimakon ka sayi kyauta mai tsada, ka kawo mata karama mara tsada sosai.
Ka lura da fuskarta: masu godiya da karamin abu sukan zama masu rikon gida kuma masu ladabi.
6. Gwajin Addini da Tarbiyya
Ka lura da yadda take ba wa sallah muhimmanci ba tare da ka matsa mata ba, sannan ka kalli yadda take mu’amala da yara ko wadanda suka kasa da ita.
Wannan na nuna ladabi, tarbiyya, da halayen aure.
Aure rami ne da ba a fita daga ciki. Idan ka yi aure da mace da ba ta da tarbiyya da halaye na kirki, zai iya zama abin damuwa a gaba.
Ka yi hankali wajen zabar matar aure domin kare kwanciyar hankalinka da gina gida mai albarka.
Allah ya albarkaci gidajenmu.
—
Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya
