Rashin wanke hannu bayan amfani da bandaki na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo yaduwar cututtuka a cikin al’umma.
Duk da sauƙin wannan aiki, mutane da yawa ba sa kula da shi yadda ya kamata.
—
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaMe Yasa Wanke Hannu Yake Da Muhimmanci?
Bayan amfani da bandaki, hannuwa na iya daukar kwayoyin cuta daga najasa. Idan ba a wanke su ba, za su iya shiga jiki ko kuma su yadu zuwa wasu mutane.
—
Illolin Rashin Wanke Hannu
1. Yaduwar Cututtuka
Kwayoyin cuta na iya shiga jiki ta:
baki
hanci
idanu
Wannan na iya jawo cututtuka daban-daban.
—
2. Ciwon Ciki
Rashin tsafta na iya jawo:
gudawa
amai
ciwon ciki
—
3. Kamuwa da Infection
Kwayoyin cuta na iya haddasa infection a jiki, musamman idan an taba abinci ba tare da tsafta ba.
—
4. Yaduwa ga Sauran Mutane
Idan ka taba:
abinci
kofa
kayan aiki
ba tare da wanke hannu ba, zaka iya yada cuta ga wasu.
—
5. Rage Kariyar Jiki
Yawan kamuwa da cuta na iya raunana garkuwar jiki (immune system).
—
Yadda Ya Kamata A Wanke Hannu
A yi amfani da ruwa da sabulu
A goge hannuwa sosai na akalla dakika 20
A wanke tsakanin yatsu da ƙarƙashin farce
A busar da hannu da tsafta
—
Wanke hannu da sabulu bayan fita daga bandaki ba ƙaramin abu bane.
Yana daga cikin manyan hanyoyin kare lafiyar kai da ta al’umma gaba ɗaya.
—
Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya
