GA ABIN DA YA KAMATA KA SANI GAME DA MALTINA DA PEAK MILK!

Maltina da Peak Milk na daga cikin abubuwan sha da mutane da dama suke amfani da su yau da kullum, musamman wajen karin kumallo ko hada drinks masu dadi.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Amma mutane da yawa basu san wasu muhimman abubuwa game da su ba.

Menene Maltina?

wani abin sha ne da aka yi daga malt, wanda baya dauke da giya. Yana dauke da sinadarai masu bada kuzari kamar carbohydrates, vitamins da wasu minerals da jiki ke bukata.

Wasu daga cikin amfanin Maltina sun hada da:

  • Samar da kuzari ga jiki
  • Taimakawa wajen rage gajiya
  • Dauke da wasu vitamins masu amfani ga lafiya
  • Yana bada dandano mai dadi musamman idan an sanyaya shi

Sai dai yawan shansa na iya kara sugar a jiki saboda yana dauke da sukari mai yawa.

Menene Peak Milk?

kuwa madara ce mai dauke da sinadarai masu gina jiki kamar:

  • Calcium domin karfin kashi da hakora
  • Protein domin gina jiki
  • Vitamins masu amfani ga lafiya
  • Fats da suke bada kuzari

Madara na da amfani musamman ga yara, mata masu ciki da kuma masu bukatar karin kuzari.

Hada Maltina Da Peak Milk

Mutane da yawa suna hada Maltina da Peak Milk saboda dandano da kuzarin da suke bayarwa.

Wannan hadin na iya zama abin sha mai dadi da kuzari musamman lokacin zafi ko karin kumallo.

Sai dai yana da kyau a sha cikin matsakaici, musamman ga masu fama da ciwon sukari ko kiba saboda yawan sugar da calories.

Shin Yana Kara Jini?

Akwai masu cewa hada Maltina da madara yana kara jini. Duk da cewa suna dauke da wasu vitamins da minerals masu amfani, ba su kadai ne maganin karancin jini ba.

Cin abinci mai gina jiki da samun shawarar likita na da muhimmanci idan akwai matsalar rashin jini.

Maltina da Peak Milk abubuwa ne masu amfani idan aka sha su yadda ya kamata.

Suna samar da kuzari da wasu sinadarai masu anfani ga jiki, amma yana da kyau a guji wuce gona da iri domin kare lafiya.

Allah ya bamu lafiya mai anfani.

Karin Bayani Anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *