Episode 2 — Bayan Na Bi Saurayi Na Hotel 😭💔
Lokacin da na ga hotel din, gaba daya jikina ya yi sanyi. Ban taba shiga irin wannan waje da namiji ba a rayuwata. Na tsaya ina kallon Jamil cikin rudani.
Shi kuwa sai murmushi yake kamar babu komai.
Ya ce:
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa“Maryam… trust me mana. Ba zan taba cutar da ke ba.”
Kalmar “trust me” din tasa ta tsaya min a rai… saboda duk soyayyar da nake masa, har yanzu zuciyata tana bani tsoro.
Muka shiga cikin hotel din. Wurin ya yi kyau sosai, haske yana laushi, kamshin turare yana tashi a ko’ina. Amma duk da haka… zuciyata bata kwanta ba.
Da muka shiga dakin, na zauna can gefe ina wasa da yatsuna saboda tashin hankali.
Shi kuwa ya zauna kusa da ni yana kallona sosai.
Sai ya ce cikin sanyin murya:
“Maryam… kin san ina son ki ko?”
Na sunkuyar da kai ina murmushi kadan. “Na sani…”
Sai ya matsa kusa dani sosai har na fara jin bugun zuciyata yana karuwa.
Ya kama hannuna a hankali.
“Tun ranar da na hadu da ke… ban taba jin son wata yarinya kamar ki ba.”
Wallahi lokacin maganganunsa suna shiga raina sosai. Na ji kamar zan iya yarda da komai saboda shi.
Amma can sai ya rungume ni.
Nan take jikina ya dauki rawa.
Na ture shi kadan ina cewa: “Jamil don Allah…”
Sai ya sake kamo hannuna yana kallona cikin wani irin yanayi.
“Baby… me yasa kike tsorona haka? Ni fa mijinki ne na gaba.”
Da jin wannan kalmar, zuciyata ta sake rauni.
Sai ya kara matsowa yana kokarin sumbatata…
Nan take na mike tsaye da sauri.
“Jamil wannan ba dai-dai bane!”
Fuskarshi ta canza kadan.
Ya ce:
“Maryam kina nufin baki yarda dani bane har yanzu?”
Na ce: “Ba haka bane… amma bana son muyi abin da zan yi nadama.”
Na lura ya fara bacin rai.
Sai ya mike yana tafiya cikin dakin kamar wanda yake kokarin danne fushi.
Can kuma ya dawo kusa dani ya ce cikin murya mai nauyi:
“To idan kina sona… ki nuna min.”
Wallahi kalmar ta girgiza ni.
Na ji hawaye sun taru a idona. Ban taba tunanin ranar da zan shiga irin wannan jarabawa ba.
Nan take na dauki jakarta da sauri na nufi kofa.
Ya ce:
“Maryam tsaya mana!”
Amma ban saurare shi ba. Na bude kofar na fita da gudu zuciyata tana bugawa kamar zata fito.
Ina fita corridor din hotel din, na ji muryarsa daga baya yana cewa:
“Wallahi Maryam… idan ba yau ba, zan sake dauko ki… kuma ranar bazaki kubuta ba.”
(To Be Continued… 😭🔥 Episode 3)
