DAGA cikin ɗakin, na jiyo muryar matata tana cewa:
“Don Allah, ka nutsu. Muyi komai a hankali, babu wata matsala…”
Na tsaya cak a bakin ƙofar ɗakin zuciyata na bugawa da ƙarfi. Ban taɓa jin muryarta cikin irin wannan salo ba. Tausasawa da sanyin murya irin wanda ke sa zuciyar namiji ta narke kamar ƙanƙara a rana.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaA hankali na tura ƙofar na shiga. Hasken fitilar ɗakin ya haskaka kyakkyawar fuskarta.
Ta zauna a bakin gado cikin wata doguwar riga mai laushi, ƙamshin turarenta na cika ɗakin kamar aljanna.
Ta ɗago idanunta tana kallona tare da murmushi mai cike da so da shauƙi.
“Ka zo mana…” ta faɗa cikin sanyin murya.
Na ƙarasa kusa da ita ina jin duk wani gajiya na rana yana gushewa. Hannunta ta kamo cikin natsuwa, ta ɗora kanta a kafaɗata.
“Na fahimci kana cikin damuwa yau,” ta raɗa a kunnuwana. “Amma ina son ka sani… duk lokacin da kake tare da ni, baka kaɗai bane.”
Maganganunta sun ratsa zuciyata kai tsaye. Na shafa gefen fuskarta cikin kulawa, ita kuma ta lumshe idanu tana murmushi.
“Kin san kina da wata hanya ta musamman da kike sata mutum mantawa da komai?” na tambaya.
Ta ɗan cije lips ɗinta cikin salon tsokana kafin tace:
“Toh wa ya ce bana son ganin mijina yana murmushi?”
Dariya muka yi tare. Na rungumeta a hankali, jikinta mai dumi yana ƙara min nutsuwa.
Ta ɗago kanta tana kallona kai tsaye cikin idanuwana, sannan ta ce:
“Soyayya ba wai magana kawai bace… kulawa ce, fahimta ce, da yadda mutum yake sa ɗan uwansa jin ana sonsa.”
Na sumbaci goshinta cikin tausayi. Lokacin ne na gane cewa ba kyau kaɗai ke sa namiji ya kamu da mace ba… akwai natsuwa, kulawa da irin yadda take sa zuciyarsa jin aminci.
A wannan daren, ɗakinmu ya cika da dariya, soyayya da kalaman da suka ƙara haɗa zukatanmu fiye da da.
Wasu lokutan, ƙaramin murmushi daga wanda kake so… yafi kowace kyauta daraja.
