Hausa News
Shin Da Gaske Atiku Ya Aje Siyasa

Shin Da Gaske Atiku Ya Aje Siyasa
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar kuma jagora a jam’iyyar ADC, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa ya yanke shawarar janyewa daga harkokin siyasa.
Jaridar Daily ta ambato ofishin Atiku na Abuja, na zargin hannun gwamnatin Nijeriya a kirkirar labarin.
A cewar sa, duk wani labari game da taron da ya yi da masu ruwa da tsaki na ADC, inda ake zargin ya yanke shawarar yin ritaya, ƙarya ce kawai kuma an tsara ta ne don ruɗani da ɓata ƙoƙarinsa na siyasa a kasar.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya jaddada cewa irin wannan shawara za a sanar da ita ne ta ofishinsa kawai ba ta hanyoyin jita-jita ko kafafen sada zumunta ba.