Fitar ruwa daga farji abu ne da ke faruwa ga kowace mace.

Amma yana da muhimmanci a san bambanci tsakanin ruwan da yake na al’ada da wanda ke nuna matsalar infection.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

1. Ruwan Farji na Al’ada (Normal Discharge)

Wannan ruwa yana da amfani sosai, domin yana taimakawa wajen tsaftace farji da kare jiki daga kwayoyin cuta.

Yaya Yake?

Launi: Fari ko mai ɗan haske (clear)

Kamshi: Ba shi da wari mai muni

Kauri: Siriri ko ɗan kauri kaɗan

Lokaci: Yakan ƙaru lokacin ovulation ko kafin al’ada

Alamomi: Ba ya kawo ƙaiƙayi ko zafi

Wannan alama ce ta lafiya, ba cuta ba.

2. Ruwan Farji Saboda Infection

Wannan yana nuna cewa akwai matsala a jiki, yawanci sakamakon ƙwayoyin cuta.

Alamominsa:

Launi: Rawaya, kore, ko fari mai kauri kamar madara

Kamshi: Wari mai muni (wani lokaci kamar kifi)

Ƙaiƙayi ko zafi a farji

Jin zafi yayin fitsari ko saduwa

Kumburi ko ja a wajen farji

Abubuwan Da Ke Jawo Infection

Rashin tsafta

Yawan amfani da sabulu mai sinadarai masu ƙarfi

Saduwa ba tare da kariya ba

Sauyin hormone

Shan wasu magunguna (musamman antibiotics)

Yaushe Ya Kamata A Ga Likita?

Idan ruwan ya canza launi ko wari

Idan kina jin ƙaiƙayi ko zafi

Idan yana hana ki jin daɗin rayuwa

Yadda Za Ki Kare Kanki

Ki riƙa tsafta amma ba da yawa ba (over-washing)

Ki sa tufafin ciki masu tsabta, musamman na cotton

Guji amfani da sinadarai masu ƙarfi a farji

Ki kula da saduwa cikin kariya


Sanin bambanci tsakanin ruwan farji na al’ada da na infection yana taimaka wa mace wajen kula da lafiyarta da wuri.

Duk wani canji da ba a saba gani ba yana bukatar kulawa da bincike.

Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *