ALAMOMIN DA KE NUNA CIKIN MACE TA SHIGA JUNA BIYU (PREGNANCY)

Akwai wasu sauye-sauye da jikin mace ke fara nunawa idan ta samu ciki. Sau da yawa wasu mata suna iya fahimta tun kafin su je asibiti ko su yi gwajin pregnancy test, saboda alamomin suna fitowa a fili.

Idan kina lura da jikinki kuma kina ganin wasu daga cikin wadannan canje-canjen, akwai yiwuwar kina dauke da juna biyu. Amma duk da haka, tabbatarwa ta karshe tana bukatar gwaji ko ganin likita.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

1. Daukewar al’ada (Menstruation)
Idan jinin haila ya tsaya kwata-kwata a lokacin da aka saba gani, yana iya zama alamar ciki.

2. Yawan jin amai ko tashin zuciya
Mace na iya fara jin tashin zuciya ko amai musamman da safe.

3. Jin gajiya da kasala da safe
Wasu mata na jin jikinsu yana yin zafi-zafi ko kasala tun farkon safe.

4. Sauyin fata da nauyi
Fata na iya yin haske ko laushi, sannan mace ta fara yin kiba kadan.

5. Jin warin abubuwa da yawa fiye da da
Warin wasu abubuwa na iya fara damun mace fiye da yadda ta saba.

6. Yawan sha’awar wani abu (craving)
Mace na iya fara sha’awar wasu abinci ko abubuwa, kuma rashin samun su na iya bata mata rai.

7. Sauyin nono (nipple)
Nonuwa na iya yin duhu kadan, su kumbura ko su yi zafi kadan.

8. Yawan fitsari
Mace na iya fara shiga bandaki akai-akai fiye da yadda ta saba.

9. Sauyin yanayi da hali
Zafin rai, damuwa ko canjin mood na iya yawaita saboda sauyin hormones.



Wadannan alamomi na iya nuna yiwuwar ciki, amma ba tabbas bane 100%. Hanya mafi inganci ita ce yin pregnancy test ko zuwa asibiti domin tabbatarwa.


Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *