Ba girma da shekaru kawai ake auna shi ba…
gaskiyar girma tana fitowa ne a hali, tunani, da yadda kake tafiyar da rayuwarka.
Ga wasu alamomi da za su iya nuna har yanzu baka kai ga cikakken girma ba:
—
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa1. Kana Gudun Ɗaukar Alhaki
kana son a riƙa yi maka komai
kana guje wa nauyin rayuwa
• Girma yana nufin ka ɗauki alhakin kanka.
—
2. Kana Yin Fushi da Sauri
ƙananan abu na ɓata maka rai
baka iya sarrafa zuciyarka
• Mutum mai girma yana da haƙuri da nutsuwa.
—
3. Kana Zargin Kowa Sai Kanka
idan abu ya lalace, kana dora laifi a kan wasu
baka iya ɗaukar kuskurenka
• Girma yana farawa da gaskiya da kai.
—
4. Rashin Tsari a Rayuwa
baka da buri ko tsari
rayuwarka tana tafiya ba tare da manufa ba
• Mutum mai girma yana da direction.
—
5. Kana Neman Jin Daɗi Kawai
duk abin da kake yi don nishaɗi ne
baka son wahala ko ƙoƙari
• Girma yana buƙatar sadaukarwa.
—
6. Kana Dogara da Ra’ayin Mutane
abin da mutane suka ce ne ke tafiyar da kai
baka da tsayayyen matsayi
• Girma yana nufin ka san kanka.
—
7. Rashin Koyon Darasi daga Kuskure
kana maimaita kuskure
baka ɗaukar darasi
• Mutum mai girma yana gyara kansa.
—
8. Kana Gudun Wahala
baka son ƙoƙari
kana son sakamako cikin sauƙi
• Rayuwa tana buƙatar juriya.
—
Darasi
Girma ba yana nufin shekaru ba ne…
yana nufin:
yadda kake tunani
yadda kake yanke hukunci
yadda kake tafiyar da rayuwarka
—
Gaskiyar Magana
Mutum na iya girma da shekaru amma halinsa ya tsaya a yara.
—
Idan ka ga wasu daga cikin waɗannan alamomi a kanka, kada ka ji tsoro — ka fara gyara kanka a hankali.
Girma tafiya ce, ba abu ne da ke faruwa a rana ɗaya ba.
Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya
