A fannin ilimin psychology, wasu samari suna nuna halin da ake kira avoidant attachment.
Wannan hali yana faruwa tun daga ƙuruciya, idan mutum bai saba da kusanci ko nuna soyayya ba.
Saboda haka, duk lokacin da ya shiga relationship, zuciyarsa na ƙoƙarin kare shi ta hanyar nisanta shi, ko da kuwa yana son wacce yake tare da ita.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa1. Rashin Kwarewa Wajen Sarrafa Motsin Zuciya
Wasu maza ba su da kwarewa wajen sarrafa motsin zuciyarsu. Idan soyayya ta fara zurfi, sai su ji wani irin nauyi ko rikicewa a zuciya.
Maimakon su fahimci abin da suke ji, sai su fara neman hanyar fita.
Wannan ne yasa zaka ga suna cikin soyayya amma zuciyarsu na neman gudu.
2. Tasirin Tarbiyya da Al’ada
A wasu lokuta, tarbiyya da al’ada na taka rawa wajen yadda namiji ke nuna kulawa.
An saba koyar da namiji ya kasance mai tauri, kada ya nuna rauni ko yawan kulawa.
Wannan yana sa ya kasa nuna soyayya yadda ya kamata, koda zuciyarsa cike take da so. Sai mace ta ɗauka cewa baya sonta, alhali yana so amma bai san yadda zai nuna ba.
3. Rikicin Zuciya da Tunanin Namiji
Abu mafi ban mamaki shi ne, irin waɗannan mutanen idan suka kamu da soyayya ta gaskiya, sukan fi kowa shan wahala.
Domin suna shiga rikici tsakanin zuciyarsu da tunaninsu: wani ɓangare yana son kusanci, wani kuma yana tsoron hakan. Wannan rikici ne ke sa su kasa samun kwanciyar hankali a soyayya.
4. Magance Matsalar Avoidant Attachment
Ba duk wanda baya kula da mace bane yana da aljanu. Mafi yawa, wasu kawai suna fama da abin da ke cikin zuciyarsu ne.
Hanyoyin magance wannan matsala sun hada da:
Sanin hali da fahimtar kanka: Namiji ya san yadda halinsa yake shafar soyayya.
Neman shawarwari daga masanan psychology:
Hakan zai taimaka wajen koyon yadda zai nuna soyayya da kusanci.
Fara da ƙananan matakai:
Nuna kulawa a hankali da yin magana akai-akai zai taimaka wajen gina kwarin gwiwa.
Hadin kai da juna: Mace da namiji su fahimci juna, su yi hakuri, kuma su yi aiki tare don gyara kuskuren da ke hana cikakken kulawa.
Babu wanda yake son cutar da abokin rayuwarsa.
Rashin iya kula da mace sau da yawa ba saboda rashin so bane, amma saboda abubuwan da suka shafi halayyar mutum da tarbiyya.
Fahimtar avoidant attachment, da neman hanyoyin magance shi, zai taimaka wajen gina soyayya mai ƙarfi, jin daɗi, da kwanciyar hankali tsakanin ma’aurata.
Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya
