Girmamawa ba a ba ka shi kyauta… ana samun sa ne daga yadda kake tafiyar da kanka.
Wasu halaye na iya sa mace ta fara raina namiji ba tare da ya lura ba.
Ga abubuwa guda 5 da ke jawo hakan:
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa—
1. Rashin tsayawa kan magana
yau ka ce abu, gobe ka canza
ba ka cika alkawari
Idan namiji ba shi da kalma, mace ba za ta ɗauke shi da muhimmanci ba.
—
2. Nuna buƙata sosai (too desperate)
kullum kai kake nema
ba ka da iyaka
kana nuna kamar ba za ka iya rayuwa ba tare da ita ba
Wannan yana rage darajar ka a idonta.
—
3. Rashin kulawa da rayuwarka
babu aiki ko buri
babu ci gaba
Mace tana girmama namiji mai direction a rayuwa.
—
4. Rashin iya yanke hukunci
komai sai ka tambaye ta
ba ka da tsayayyen ra’ayi
Namiji mai rauni a yanke hukunci yana rasa girmamawa.
—
5. Rashin girmama kanka
ka yarda da komai
baka da iyaka
ana raina ka, ka yi shiru
Idan ba ka girmama kanka ba, babu wanda zai girmama ka.
—
Darasi
Girmamawa yana farawa ne daga kai.
Yadda kake tafiyar da kanka shi ne yadda mutane za su ɗauke ka.
—
Idan kana son mace ta girmama ka:
ka zama mai tsari
ka tsaya kan magana
ka gina kanka
—
Tambaya Ga Masu Karatu:
• Wanne daga cikin waɗannan kake ganin ya fi jawo rashin girmamawa?
Danna Nan Don Samun Wasu Sirrikan Ma’aurata Da Soyayya
