Abin Da Doka Ta Ce Akan Budurwar Da Ta Amince Da Saurayi Amma Aka Yada Bidiyon 😳⚖️
Ga Bayani Mai Muhimmanci 👇
A yanzu ana yawan samun rahotannin wasu matasa da suke shiga soyayya har a kai ga ɗaukar bidiyo masu zaman kansu, daga baya kuma sai a yada su a social media.
Mutane da yawa suna tambaya: shin idan budurwa ta yarda da saurayi, hakan yana nufin yana da damar yada bidiyon?
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa⚖️ Abinda Doka Ta Ce:
A ƙarƙashin dokokin Najeriya, musamman dokar Cybercrimes Act, yaɗa bidiyo ko hotunan sirri ba tare da yardar wanda ke ciki ba babban laifi ne.
Ko da:
- sun amince da soyayya
- ko sun aikata abin da suka aikata da yardar juna
hakan ba ya nufin an yarda:
- a ɗauki bidiyo
- ko a yada shi a internet
⚠️ Wanda Aka Kama Zai Iya Fuskantar:
- Dauri a gidan yari
- Tara mai tsanani
- Ko duka biyun tare
⚠️ Darasi Ga ‘Yan Mata:
- Kada ku yarda a ɗauki videos masu zaman kansu
- Ku kula da wanda kuke yarda da shi
- Duk abin da ya shiga internet yana iya zama da wahalar gogewa
⚠️ Darasi Ga Samari:
Namiji mai mutunci baya amfani da sirrin mace wajen cutar da ita ko neman suna.
🛑 A ƙarshe:
Kare mutuncin mutane da sirrinsu yana da muhimmanci sosai. Social media ba wajen rusa rayuwar mutane bane.
