Sakonnin Soyayya Guda 10 Masu Daɗi Da Za Ka Turawa Masoyiyarka
1.
“Duk ranar da ban ji muryarki ba, ranar tana min kamar ba ta cika ba.”
2.
“Ke ce kwanciyar hankalina, duk lokacin da nake tare da ke zuciyata tana samun nutsuwa.”
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa3.
“Bana buƙatar mutane da yawa su faranta min rai, murmushinki kaɗai ya isa ya canza yanayina.”
4.
“Wani lokacin ina mamakin yadda kika shiga raina har na kasa daina tunaninki.”
5.
“Idan soyayya laifi ce, to ni a shirye nake in ci gaba da aikata ta saboda ke.”
6.
“Ko da duniya za ta canza, akwai abu ɗaya da ba zai taɓa canzawa ba — yadda nake son ki.”
7.
“Ke ba kawai masoyiya ta bane, ke ce farin cikin da nake nema kullum.”
8.
“Duk lokacin da kika ce kina missing ɗina, zuciyata tana jin wani irin daɗi.”
9.
“Ba kyau kawai nake gani a tare da ke ba, ina ganin mace mai kula, mai tausayi, kuma mai saka farin ciki.”
10.
“Ina son yadda kike sa ni murmushi ba tare da kin yi wani abu mai yawa ba.”
Waɗannan sakonni suna ƙara kusantar zuciya idan aka tura su a lokaci mai kyau, musamman da dare ko lokacin da take missing ɗinka.
