Kana Jin Ƙaiƙayi a Duburarka Musamman Yayin Da Ka Zo Barci? Toh Ga Abin Da Hakan Yake Nufi
Jin ƙaiƙayi a dubura musamman da dare ko lokacin kwanciya barci na iya zama alamar wasu matsaloli da ke buƙatar kulawa.
Wasu lokuta matsalar tana da sauƙin magani, amma idan aka yi watsi da ita tana iya ƙara tsananta.
Ga wasu daga cikin abubuwan da kan iya jawo hakan:
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa1. Tsutsar Ciki (Pinworm)
Wannan na daga cikin sanannun abubuwan da ke jawo ƙaiƙayi a dubura musamman da dare. Tsutsar tana yawan fitowa da daddare wanda hakan ke haddasa ƙaiƙayi mai tsanani.
2. Rashin Tsafta
Ragowar datti ko zufa a wajen dubura na iya haddasa kaikayi da rashin jin daɗi.
3. Amfani Da Sabulai Ko Sinadarai Masu Karfi
Wasu sabulai, creams ko turare na iya tayar da kaikayi a fata mai laushi.
4. Basir Ko Kumburin Dubura
Wasu matsaloli kamar basir na iya sa mutum jin kaikayi, ciwo ko rashin jin daɗi.
5. Cutar Fungal Ko Infection
Wasu infections a fata na iya haddasa kaikayi musamman idan wajen yana yawan danshi.
Abin da ya kamata ka yi:
• Ka kula da tsaftar jikinka sosai
• Ka guji amfani da abubuwan da ke tayar da kaikayi
• Ka rika canza kayan ciki akai-akai
• Idan matsalar ta yi tsanani ko ta dade, ka je asibiti domin duba lafiya
Yin watsi da matsalar ba shi da kyau musamman idan tana maimaituwa ko tana hana ka samun nutsuwar barci.
