Abinda Yasa Kuke Jin Zafi Lokacin Fitsari
Jin zafi yayin fitsari wata matsala ce da mutane da dama suke fuskanta, amma wasu kan yi shiru saboda kunya ko rashin sanin abin da ke haddasa hakan.
Wannan matsala na iya faruwa ga maza ko mata, kuma tana iya zama alamar wata cuta ko matsalar lafiya da ke bukatar kulawa.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaGa wasu daga cikin abubuwan da ka iya haddasa jin zafi lokacin fitsari:
1. Cutar Fitsari (UTI)
Wannan ita ce daya daga cikin manyan dalilan jin zafi yayin fitsari. Kwayoyin cuta kan shiga mafitsara ko hanyoyin fitsari su haddasa kaikayi da zafi.
2. Rashin Shan Ruwa Isasshe
Idan mutum baya shan ruwa sosai, fitsari kan yi kauri kuma hakan na iya haddasa zafi yayin fita.
3. Cutar Sanyi Ko Infection
Wasu cututtuka da ake dauka ta hanyar jima’i ko rashin tsafta kan haddasa zafi da kaikayi yayin fitsari.
4. Dutse A Mafitsara Ko Koda
Samuwar ƙananan duwatsu a hanyoyin fitsari na iya haddasa tsananin zafi yayin fitsari.
5. Amfani Da Sinadarai Masu Karfi
Wasu sabulai, turare ko kayan tsafta masu sinadarai masu karfi kan jawo kaikayi da kumburi a al’aura.
6. Rauni Ko Goge-Goge
Yawan goge al’aura da karfi ko samun rauni a wajen na iya sa fitsari ya rika haddasa zafi.
7. Matsalar Prostate Ga Maza
Ga wasu maza musamman masu shekaru, kumburin prostate kan kawo matsalar fitsari da zafi.
Alamomin Da Ya Kamata A Lura Da Su
- Jin zafi mai tsanani yayin fitsari
- Fitsari mai wari ko canjin launi
- Jinin fitsari
- Yawan zuwa fitsari ba tare da yawa ya fito ba
- Zazzabi ko ciwon mara
Abin Da Ya Kamata A Yi
- A yawaita shan ruwa
- A kula da tsafta
- A guji amfani da sinadarai masu karfi a al’aura
- A je asibiti idan matsalar ta yi tsanani ko ta dade
Lafiya na da muhimmanci sosai. Duk lokacin da kuka lura da wata matsala da ba ta sabawa ba, yana da kyau a nemi shawarar likita domin samun magani cikin lokaci.
