“Na Yi Kuskuren Soyayya Da Mutumin Da Bai Taba Nufin Aurena Ba” 😭💔

Sunana Fatima Abdullahi… kuma gaskiya akwai wani irin ciwo da soyayya take bari a zuciya idan ka so mutum fiye da yadda yake sonka.

Na hadu da Ahmad a lokacin da ban taba tunanin zan fada soyayya ba. Yadda yake min magana, yadda yake kula dani, da yadda yake nuna kamar ni kadai ce a rayuwarsa… duk sun sanya ni yarda da shi gaba daya.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Kullum sai ya kira ni da:

“Matar aurena.” “Uwargida ta.” “Mace ta ta har abada.” ❤️

Wallahi duk lokacin da yake fada min haka, zuciyata tana narkewa.

Na fara ganin rayuwata tare da shi. Har sunayen yaranmu wani lokaci nake tunani idan ina kwance 😭❤️

Abokaina suna cewa:

“Fatima ki kula kada ki cika trusting dinsa.”

Amma ni bana ganin laifinsa.

Saboda idan mutum yana cikin soyayya… wani lokaci baya ganin jan flags.

Ahmad ya saba bani attention sosai. Duk inda yake sai ya fada min. Idan ban ji muryarsa ba ko rana daya, sai ya ce:

“Bana iya zama babu ke.”

Wannan kalmomin ne suka kashe min tunani gaba daya.

A hankali na fara daukarsa kamar mijina na gaskiya.

Ranar daya taba cewa:

“Fatima wallahi idan ba ke ba… bana ganin wace zan aura.”

Sai da na yi kuka saboda farin ciki.

Ban san cewa ni kadai ce nake serious da soyayyar ba…

Lokaci yana tafiya, soyayyarmu tana kara karfi. Har mutane sun fara saninmu tare.

Amma daga baya na fara lura yana canzawa.

Reply dinsa ya ragu.

Kiransa ya daina yawa.

Idan na tambaye shi sai yace:

“Aiki ne kawai yana damuna.”

Na yarda… saboda ina son sa.

Wata rana da dare ina online, sai wata kawata ta turo min screenshot.

Da farko ban gane ba.

Amma da na bude…

Sai naga Ahmad yana posting hoton wata yarinya a status dinsa tare da caption:

“My future wife.” 💔

Wallahi jikina yayi sanyi.

Na kasa numfashi na wasu dakiku.

Na kira shi nan take… amma bai daga ba.

A wannan daren ban yi bacci ba. Hawaye kawai nake yi ina tuna duk promises dinsa.

Washegari da safe ya kira ni.

Da na daga, kafin ma yayi magana sai nace cikin kuka:

“Ahmad… ni ba ka taba nufin aura ba ko?”

Sai yayi shiru.

Shirun nan nasa ya karya min zuciya fiye da kowanne karya.

Daga baya kawai yace:

“Fatima… ban taba son ki ki dauki komai serious haka ba.”

Wallahi a lokacin na ji kamar duniya ta tsaya.

Ashe duk soyayyar da nake gani… wasa ne kawai a wajensa 😭💔

A ranar na gane cewa:

“Abu mafi zafi ba rabuwa bane… sai ka so mutum da zuciya daya alhali shi ko kadan bai taba shirya zama naka ba.” 🥺

Duba Karin Bayani A Nan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *