Mutane Da Yawa Basa Barin Soyayya Saboda Sun Daina So… Suna Barinta Ne Saboda Sun Gaji Da Jin Kamar Ba’a Ganinsu
Akwai wani irin ciwo da baya bayyana a fuska.
Ba ciwon cin amana bane… Ba kuma ciwon rashin soyayya kai tsaye bane…
Sai dai ciwon da mutum yake ji idan yana cikin soyayya amma har yanzu yana jin shi kadai ne.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaWasu mutane basa fita daga relationship saboda sun daina son partner dinsu. A’a.
Har yanzu suna son mutum din… Har yanzu suna tunaninsa… Har yanzu zuciyarsu tana manne da shi…
Amma sun gaji.
Sun gaji da jin kamar babu wanda yake lura da kokarinsu.
Sun gaji da kasancewa su kadai ke kokarin gyara komai. Sun gaji da boye damuwa yayin da babu wanda yake tambayar su “lafiya kuwa?”
Soyayya Bata Mutuwa Lokaci Daya
Yawanci soyayya bata karewa a rana daya.
Tana mutuwa ne a hankali…
Lokacin da:
- mutum yake magana amma ba’a saurare shi
- yake kuka amma ana ganin overreacting yake
- yake kokarin nuna kulawa amma ana daukarsa normal
- yake bukatar attention amma ana masa ignoring
A hankali zuciya tana fara gajiya.
Mutum zai fara daina explaining kansa. Zai fara yin shiru akan abubuwan da suke bata masa rai.
Ba saboda komai ya gyaru ba… Sai saboda ya fara yarda cewa ko yayi magana babu wanda zai fahimce shi.
Emotional Neglect Yafi Ciwo Fiye Da Fada
Wasu suna tunanin relationship mai matsala shine wanda ake yawan fada.
A’a.
Akwai relationship da babu fada sosai… amma akwai nisa a zuciya.
Kana tare da mutum amma baka jin connection. Kana magana amma baka jin ana fahimtar ka. Kana cikin soyayya amma kana jin loneliness.
Wannan shine emotional neglect.
Kuma yana daya daga cikin abubuwan da suke kashe soyayya cikin nutsuwa.
Domin zuciya tana bukatar:
- kulawa
- empathy
- sauraro
- appreciation
- emotional presence
Ba kudi kadai bane soyayya. Ba posting ba ne. Ba “I love you” kawai bane.
Wani lokaci mutum yana bukatar kawai a lura da canjin mood dinsa. A tambaye shi dalilin shirunsa. A nuna masa cewa akwai wanda yake ganinsa da gaske.
Wasu Mutane Sun Kware Wajen Boye Gajiyarsu
Abin tausayi shine… mutane da yawa suna murmushi yayin da zuciyarsu ta gaji.
Zaka ga mutum yana replying normally… yana posting… yana dariya…
Amma a ransa ya dade da jin kamar: “Nobody really sees me.”
Saboda haka idan wata rana suka fara distancing kansu… ko suka daina kokarin da suke yi a baya… ba koyaushe bane saboda sun canza.
Wata rana kawai zuciyarsu ta gaji da rokon attention da understanding.
Soyayya Tana Bukatar A Ji Ka
Daya daga cikin manyan abubuwan da ke sa relationship ya dade shine: mutum ya ji cewa ana ganinsa.
Ana lura da feelings dinsa. Ana girmama emotions dinsa. Ana sauraron damuwarsa.
Idan mutum ya dade yana jin kamar invisible… zai iya kasancewa tare da kai amma zuciyarsa ta fara yin nisa.
Kuma idan zuciya tayi nisa… komai na iya fara rushewa a hankali.
Karshe
Idan kana son soyayya ta dore… kada ka tsaya wajen nuna love kawai.
Ka koya:
- sauraro
- lura da details
- tambayar “kana lafiya?”
- appreciation
- emotional support
Domin wani lokacin… abinda mutum yake bukata ba manyan abubuwa bane.
Yana bukatar kawai ya ji cewa: “Akwai wanda yake gani na da gaske.”
