🛑 SIRRIN BUDURCI: SHIN HYMEN NA IYA YAGEWA BA TARE DA SADUWA BA?

Mutane da yawa suna daukar cewa duk mace da ba ta zubar da jini a daren farko to lallai ta taba sanin namiji.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Amma a bangaren kimiyyar lafiya, wannan fahimta ba koyaushe take zama gaskiya ba.

A yau za mu duba wasu daga cikin abubuwan da ka iya sa fatar budurci wato Hymen ta yage ko ta sauya ba tare da mace ta yi jima’i ba.

Menene Hymen?

Hymen wata siririyar fata ce da ke bakin farjin mace. Yanayinta yana bambanta daga mace zuwa mace.

Wasu suna da ita mai kauri, wasu kuma siririya ce sosai.

A wasu matan ma, ana iya haihuwarsu ba tare da wannan fatar ba.

1. Wasanni Da Ayyukan Karfi

Masana lafiya sun bayyana cewa wasu wasanni ko ayyukan motsa jiki na iya sa Hymen ta yage musamman idan tana da siranci.

Daga cikin abubuwan da ka iya haddasa hakan akwai:

  • Hawan doki
  • Hawan keke
  • Tsalle-tsalle da gudu mai karfi
  • Wasannin Gymnastics
  • Faduwa a kan wani abu mai tsini

Wadannan abubuwa na iya jawo matsin lamba ko jijjiga da zai taba fatar.

2. Yanayin Halitta

Yanayin halittar mace yana taka muhimmiyar rawa wajen yadda Hymen take.

Rashin Hymen Tun Haihuwa

Akwai wasu mata da ake haifarsu ba tare da Hymen ba kwata-kwata.

Elastic Hymen

Wasu kuma suna da Hymen mai laushi sosai, ta yadda ko an yi saduwa da su ba sai ta yage ko ta sa jini ya fito ba.

3. Amfani Da Wasu Kayan Tsafta

A wasu lokuta, amfani da wasu kayan tsafta kamar audugar haila da ake sakawa a ciki (tampons) na iya taba Hymen musamman idan ba a saba amfani da su ba.

Haka kuma wasu binciken lafiya da likitoci ke yi a mahaifa kan iya taba wannan fatar.

4. Kuskure Wajen Tsafta

Wasu mata kan yi amfani da yatsa ko wani abu wajen tsaftace gabansu da karfi yayin haila, wanda wani lokaci kan iya taba Hymen ba tare da sun sani ba.

Shin Rashin Jini Na Nufin Ta Taba Namiji?

Amsar ita ce a’a. Rashin jini a daren farko ba cikakkiyar hujja ba ce cewa mace ta taba yin jima’i. Jikin mata ya bambanta, haka kuma yanayin Hymen dinsu.

Shi ya sa masana lafiya suke jan hankali ga al’umma da su guji gaggawar yanke hukunci ba tare da cikakken ilimi ko bincike ba.

Ilimi yana taimakawa wajen kare mutuncin mata da kuma rage rashin fahimta a tsakanin ma’aurata da iyalai.

Yana da muhimmanci mu fahimci cewa ba kowace mace ce za ta zubar da jini a daren farko ba, kuma hakan kadai ba hujja ba ce ta yanke hukunci kan budurci.

Allah ya kara mana ilimi mai anfani da fahimtar juna.

Shiga Nan Domin Karin Bayani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *