Kwaroron Roba (Condom) Ba Alamar Iskanci Bane: Muhimmiyar Wayar Da Kai Ga Jama’a
A kullum jami’an lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya suna kokari wajen wayar da kan al’umma kan yadda za su kare lafiyarsu daga cututtuka masu yaduwa ta hanyar saduwa da kuma hanyoyin tsara iyali cikin aminci.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaDaya daga cikin hanyoyin kariya da masana lafiya suka fi bada shawara a kai shi ne amfani da kwaroron roba (Condom), musamman ga ma’aurata ko mutanen da kwararrun jami’an lafiya suka ba shawarar amfani da shi domin kare lafiya.
Masana sun bayyana cewa amfani da kwaroron roba yadda ya kamata na taimakawa wajen rage yaduwar wasu cututtuka masu hadari kamar:
• HIV/AIDS
• Gonorrhea
• Syphilis
• Chlamydia
• Hepatitis B
• Trichomoniasis
Haka kuma, yana taimakawa wajen tsara tazarar iyali cikin sauki da kariya.
Sai dai duk da wannan muhimmanci, har yanzu mutane da yawa suna jin kunya ko tsoron zuwa siyan condom saboda yadda wasu ke kallon duk mai siya a matsayin “dan iska” ko mutum mara tarbiyya.
Masana lafiya sun ce irin wannan tunani na iya hana mutane samun kariyar da suke bukata, musamman wadanda aka ba shawarar amfani da shi domin lafiyarsu da ta iyalansu.
A gaskiya, ba duk masu amfani da condom bane masu aikata abin da bai dace ba.
Akwai ma’aurata da dama da jami’an lafiya ke ba shawarar amfani da shi saboda kariya daga cututtuka ko tsarin iyali.
Saboda haka, akwai bukatar jama’a su daina yi wa masu sayen condom kallon banza ko tozarci.
Bari mutane su iya samun kayan kariya cikin nutsuwa ba tare da tsoro ko kunyatawa ba.
Masana sun jaddada cewa kare lafiya ya fi muhimmanci fiye da yadda mutane za su yi hukunci akan wani ba tare da sanin dalilinsa ba.
Allah Ya ba mu lafiya da kariya daga dukkan cututtuka.
