Hanyoyi 5 Da Za Ka Ci Naman Sallah Ba Tare Da Cikinka Ya Lalace Ba

Lokacin Sallah mutane da yawa suna cin nama fiye da yadda suka saba, wanda wani lokacin ke janyo ciwon ciki, gudawa ko rashin narkewar abinci.

Ga wasu hanyoyi da za su taimaka maka ka ci naman Sallah cikin lafiya.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

1. Kar Ka Ci Nama Da Yawa Lokaci Guda

Yawan cin nama a lokaci ɗaya na iya janyo kumburin ciki, ciwo ko rashin narkewar abinci. Ka riƙa ci cikin gwargwado domin jikinka ya samu damar narkewa cikin sauƙi.

2. Ka Tabbatar Naman Ya Dahu Sosai

Naman da bai dahu sosai ba na iya ɗauke da ƙwayoyin cuta masu haddasa gudawa da ciwon ciki. Ka tabbatar an dafa ko an soya shi yadda ya kamata kafin a ci.

3. Ka Rage Mai Da Yaji Masu Yawa

Nama mai kitse sosai ko yaji mai yawa na iya tada ulcer, tashin zuciya da ciwon ciki. Yin anfani da matsakaicin mai da yaji zai fi lafiya.

4. Ka Ci Tare Da Kayan Lambu Da Ruwa Sosai

Shan ruwa da cin kayan lambu suna taimakawa wajen narkewar abinci da rage maƙarƙashiya. Hakan kuma yana taimakawa ciki ya ji sauƙi bayan cin nama.

5. Ka Guji Cin Tsohon Nama Da Ya Lalace

Idan aka bar nama ba tare da an adana shi da kyau ba, yana iya lalacewa ya haddasa food poisoning. Ka tabbata an ajiye naman a wuri mai sanyi kuma an dumama shi da kyau kafin a sake ci.

Lafiya ta fi komai muhimmanci a lokacin Sallah. Ku ci abinci cikin kula domin ku more bikin cikin farin ciki da lafiya.

Duba Karin Bayani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *