Lokuta 2 Da Ciki Baya Shiga Ko Da An Sadu Da Mace
Akwai lokuta da ma’aurata za su yi jima’i amma ciki bai shiga ba, duk da cewa babu wata matsala mai tsanani a tare da su.
Wannan na faruwa ne saboda yanayin jikin mace da kuma lokacin da aka yi saduwar.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaGa wasu daga cikin lokutan da yuwuwar samun ciki kan ragu sosai:
1. Bayan Lokacin Ovulation Ya Wuce
Ovulation shi ne lokacin da ƙwan mace ke fitowa domin samun damar haɗuwa da maniyyi. Wannan lokaci ne da mace ta fi samun ciki idan aka yi saduwa.
Idan kwan ovulation ya wuce kuma ƙwan ya mutu ba tare da an samu haɗuwa da maniyyi ba, yuwuwar samun ciki kan yi ƙasa sosai.
Saboda haka, ko an yi jima’i bayan kwanakin haihuwa sun wuce, akwai yiwuwar ciki ba zai shiga ba.
2. Lokacin Al’ada Ko Kusa Da Zuwa Al’ada
A mafi yawan lokuta, mace tana da ƙarancin yiwuwar samun ciki yayin al’ada ko kwanakin da suke kusa da zuwan al’ada.
Wannan saboda jikin mace baya cikin lokacin haihuwa a wannan lokaci.
Sai dai masana suna bayyana cewa hakan ba yana nufin ciki ba zai taɓa shiga ba kwata-kwata.
Wasu mata na iya samun sauyin jadawalin haila wanda zai sa ciki ya shiga ko a lokacin da ake tunanin babu yiwuwar hakan.
Abubuwan da ke iya shafar samun ciki sun haɗa da:
- Yanayin lafiyar mace da namiji
- Lokacin ovulation
- Matsalolin hormones
- Damuwa da gajiya
- Rashin ingantaccen abinci
Idan ma’aurata sun daɗe suna ƙoƙarin samun haihuwa ba tare da nasara ba, yana da kyau su ga ƙwararren likita domin duba lafiyarsu.
