Dalilan Rashin Tashin Azzakari (Erectile Dysfunction) Da Hanyoyin Magancewa: Cikakken Bayani

Maza da dama na fama da matsalar rashin tashin azzakari amma saboda kunya ko tsoro basa iya bayyana matsalar.

Wasu suna tunanin sihiri ne, wasu kuma suna ganin matsalar ba ta da magani.

Amma a gaskiya, akwai dalilai da dama da ke haddasa wannan matsala kuma mafi yawansu ana iya magance su idan an gano asalin abin da ke jawo ta.

👉 Kana son ganin cikakken bayani?

🔥 Danna nan don cigaba da karantawa

Rashin tashin azzakari na nufin lokacin da namiji baya iya samun karfin da zai ba shi damar saduwa yadda ya kamata, ko kuma karfin baya dadewa kafin a gama jima’i.

Ga Wasu Daga Cikin Dalilan Matsalar:

1. Yawan Damuwa Da Tunanin Rayuwa

Damuwa, stress, ko yawan tunani na iya rage sha’awar namiji tare da hana jini gudana yadda ya kamata zuwa ga azzakari.

2. Ciwon Suga

Masu ciwon suga suna cikin wadanda suka fi fama da matsalar rashin karfin maza saboda yadda cutar ke lalata jijiyoyin jini da nerves.

3. Hawan Jini

Hawan jini na hana jini zagayawa yadda ya kamata a jiki, wanda hakan ke kawo matsala wajen tashin azzakari.

4. Shan Sigari Da Giya

Sigari da giya suna lalata lafiyar jijiyoyin jini, kuma hakan na daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa Erectile Dysfunction.

5. Rashin Motsa Jiki

Yawan zama ba tare da motsa jiki ba yana kawo kiba da matsalolin zuciya, wanda daga baya zai iya shafar karfin namiji.

6. Rashin Isasshen Barci

Karancin barci na rage sinadarin testosterone a jiki, wanda ke da muhimmanci wajen karfin maza.

7. Amfani Da Wasu Magunguna

Akwai wasu magungunan da suke da side effects da ke haddasa rashin tashin azzakari, musamman wasu magungunan hawan jini ko damuwa.

Hanyoyin Magance Matsalar

1. Rage Damuwa

Ka rika samun hutu, ka rage yawan tunani, sannan ka guji abubuwan da ke kara stress.

2. Yin Motsa Jiki

Motsa jiki kamar tafiya, gudu ko push-up na taimakawa wajen kara zagayawar jini a jiki.

3. Gujewa Sigari Da Giya

Daina shan sigari da giya na iya taimakawa wajen dawo da karfin maza cikin lokaci.

4. Cin Abinci Mai Gina Jiki

Abinci mai kyau kamar kayan lambu, fruits, kifi da gyada na taimakawa lafiyar jiki da karfin maza.

5. Duba Likita

Idan matsalar ta yi tsanani ko ta dade, yana da kyau a ga likita domin a gano musabbabin matsalar da kuma samun maganin da ya dace.

Wasu maza suna boye matsalar ne har ta kai ga lalata zaman aurensu, alhali ana iya samun sauki idan an dauki mataki da wuri.

Duba Karin Bayani

📢 Kada ka tsaya anan!

👉 Danna nan ka ga abin da ke gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *