Yadda Za Ku Gane Kuna Warin Baki Da Yadda Za Ku Magance Shi — Asiri Rufe
Wani lokacin, rashin sani yakan sa mutum ya tsinci kansa a cikin yanayi na jin kunya ba tare da ya sani ba.
Warin baki na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke rage wa mutum kima da kwarjini a cikin al’umma.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa
Mafi yawan lokuta, mutum baya gane cewa bakinsa na wari, amma akwai wasu alamomi da hanyoyi masu sauƙi da za su iya nuna muku hakan kafin wasu su fada muku.
Alamomin Da Za Ku Gane Bakinku Na Wari
Idan kuna son sanin matsayinku, ku lura da waɗannan abubuwan:
- Kaucewar Mutane: Idan ka fura baki kana magana, sai ka ga mutane suna kaucewa ko ja da baya kadan yayin da kuke tattaunawa.
- Ɗanɗano Mara Kyau: Idan kana/kina yawan jin wani ɗanɗano mara daɗi ko mai daci a baki kusan kowane lokaci.
- Bushewar Baki: Idan baki yana yawan bushewa (Rashin isasshen yawu a baki yana haddasa wari).
- Farin Datti a Harshe: Idan harshenka yana da farin datti mai kauri a ibisansa.
- Gwajin Yatsa: Idan bayan ka/ki shafa yatsa a jikin harshe, bayan seconds kadan ka sunsuno yatsan sai kaji yana wari.
Hanyoyin Magance Warin Baki (Asiri Rufe)
Kada ku damu, idan kuna fuskantar wannan matsala, ga hanyoyi mafi sauƙi da za ku bi domin dawo da martabar bakinku da numfashi mai daɗi:
- Goge Haƙora Sau Biyu: Tabbatar kana goge haƙoranka aƙalla sau biyu a rana—safe kafin cin abinci da kuma dare kafin barci.
- Wanke Harshe: Kada ka tsaya a kan haƙora kawai, wanke harshe sosai domin shi ne babban mazaunin ƙwayoyin cuta (bacteria) da ke kawo wari.
- Mouthwash da Dental Floss: Yi amfani da ruwan kurkure baki (mouthwash) da kuma zaren cire ragowar abinci na haƙora (dental floss).
- Yawaita Shan Ruwa: Shan ruwa akai-akai yana taimakawa wajen wanke ragowar abinci da kuma hana baki bushewa.
- Rage Abubuwa Masu Wari: Takuita cin abinci masu kawo wari (kamar albasa danya ko tafarnuwa) da kuma daina shan taba sigari.
- Ziyartar Likita: A dinga zuwa asibitin haƙori domin duba lafiyar baki lokaci-lokaci.
FAZAKARWA: Idan warin bakin ya ƙi dainawa duk da tsananin tsafta, yana da kyau a gaggauta ganin likita, domin wani lokacin yana iya zama alamar wata cutar daban ta cikin jiki.
Karin Bayani A Nan
