Da Gan-Gan Samari Da ’Yan Mata Suke Yin Bidiyoyin Lalata Suna Siyarwa Don Neman Kudi… Ga Gaskiyar Da Ke Boye A Ciki 👇
A wannan zamani na kafafen sada zumunta, ana samun wasu samari da ’yan mata da suke shiga harkar yin bidiyoyin batsa domin neman kudi cikin gaggawa.
Wasu na ganin kamar hanya ce mai sauki ta samun suna ko arziki, amma a zahirin gaskiya akwai manyan illoli da hatsarori da ke tattare da wannan abu.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaMutane da dama sun shiga nadama bayan bidiyoyinsu sun yadu a duniya, domin da zarar abu ya shiga internet yana da wahalar gogewa gaba daya.

Wasu sun rasa mutuncinsu, wasu sun rasa aurensu, yayin da wasu kuma suka fada cikin damuwa da bakin ciki saboda yadda mutane suke kallonsu a rayuwa.
Abu mafi muni shi ne, mafi yawan wadanda ke anfani da irin wadannan bidiyoyi ba wai suna taimakon masu yin su bane, sai dai anfani da su domin samun kudi ko suna.
Daga karshe wanda aka dauka a bidiyon shi ne yake daukar kunya da nadama har karshen rayuwa.
Matasa su sani cewa:
- Kudi na gaggawa ba koyaushe bane alheri.
- Mutunci da darajar mutum sun fi komai muhimmanci.
- Duk abin da aka saka a internet na iya zama tarihi da ba zai goge ba.
- Akwai hanyoyi masu tsafta da mutunci na neman kudi ba tare da lalata rayuwa ba.
Iyaye kuma su kara kula da ’ya’yansu, su basu tarbiyya da shawara kafin su fada tarkon masu yaudara a social media.
Allah Ya shirya matasanmu baki daya 🤲
