Nau’o’in Panties Da Ya Kamata Kowace Mace Ta Sani Da Kuma Illolinsu
A yau, akwai nau’o’in kayan ciki na mata (panties) daban-daban, amma gaskiya ita ce ba kowace mace ce ta san bambancin su da kuma wanda ya fi dacewa da lafiyarta ba.
Wannan hoto yana nuna wasu daga cikin nau’o’in panties da ake amfani da su a yau.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawa
Na farko, akwai nau’o’i masu rufe jiki sosai kamar briefs, high rise da hipster.
Wadannan suna da anfani wajen bada kariya da kwanciyar hankali, kuma suna rage gogayya a fata.
Amma idan sun yi matse sosai ko kuma ba su da kyau a tsafta, suna iya jawo zufa da kuma kamuwa da infection.
Na biyu, akwai matsakaicin nau’i kamar bikini da low rise.
Wadannan suna da saukin sawa kuma suna bada dan iska, amma idan aka yi amfani da kayan da ba su da inganci, na iya haddasa kaikayi ko rashin jin dadi.
Na uku, akwai nau’o’in da suka fi bude jiki kamar tanga, thong da g-string.
Duk da cewa wasu na amfani da su saboda salo ko kyau, suna iya jawo matsaloli kamar:
- Saukin yada kwayoyin cuta daga baya zuwa gaba
- Karin hadarin kamuwa da infection
- Jin kaikayi ko kumburi idan an dade ana sawa
Haka kuma, panties da aka yi da kayan roba ko wadanda ba sa shakar iska (non-breathable fabrics) na iya kara hadarin zufa da wari mara dadi.
Abin da ya fi muhimmanci shi ne mace ta zabi kayan ciki masu kyau, masu tsabta, kuma wadanda ba sa matse jiki sosai.
Haka kuma, canza su akai-akai da kiyaye tsafta na da matukar muhimmanci ga lafiyar al’aura.
A ƙarshe, ba salo kadai ya kamata a duba ba, lafiya da jin dadi su ne ya kamata su zama a gaba.
