Tashen balaga wani muhimmin mataki ne a rayuwar mace, inda jiki ke fara sauyawa daga yarinya zuwa cikakkiyar mace.
👉 Kana son ganin cikakken bayani?
🔥 Danna nan don cigaba da karantawaWannan lokaci yana zuwa ne da canje-canje na jiki da na tunani, kuma yana da kyau a san alamominsa domin fahimta da shiri.
Ga wasu daga cikin manyan alamun tashen balaga a mace:
Na farko, fara girman nono. Wannan shi ne daga cikin alamomin farko da ake gani, inda nono ke fara kumbura a hankali.


Na biyu, fitowar gashi a wasu sassan jiki kamar a ƙarƙashin hannu da kuma a gabanta.
Na uku, fara zuwan jinin al’ada. Wannan yana nuna cewa jikin mace ya fara shirin daukar ciki a nan gaba.
Na hudu, sauyin siffar jiki. Kwankwaso na iya faɗaɗa, jiki ya fara samun siffar mace.

Na biyar, karin zufa da sauyin wari na jiki. Wannan na faruwa ne saboda canjin hormones a jiki.
Na shida, sauyin yanayin tunani. Yarinya na iya fara jin sabbin motsin zuciya, sauyin hali ko jin kunya fiye da da.
Na bakwai, karin tsayi da nauyi. Jiki na iya fara girma cikin sauri a wannan lokaci.
Yana da muhimmanci iyaye su rika wayar da kan ‘ya’yansu mata game da wannan mataki, su ba su kulawa da shiriya domin su fahimci abin da ke faruwa a jikinsu ba tare da tsoro ba.
A ƙarshe, tashen balaga abu ne na dabi’a da kowa ke wucewa.
Fahimta da ilimi su ne mabuɗin samun kwanciyar hankali a wannan lokaci.

8
